Najeriya za ta nemi goyon baya a yakin da take yi a yanzu haka da kungiyar Boko Haram, da kuma warware matsalar jin kai da ake fuskanta, musamman ma a yankin arewa maso gabashin kasar, a yayin babban taron Afrika da kasashen Larabawa karo na hudu da zai gudana a ranar 23 ga watan Nuwamba a birnin Malabo na kasar Guinea Equatoriale, in ji wani jami'i a ranar Litinin.
Femi Adesina, kakakin fadar shugaban kasar Najeriya, ya yi wannan furuci a cikin wata sanarwa, tare da jaddada cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai hadu tare da sauran shugabannin kasashe da gwamnatoci na kasashen Afrika da yankin Gulf.
Wannan taro zai cimma wata sanarwar Malabo, da kuma shirin aiki na shekarar 2017 zuwa shekarar 2019, da aka kebe wajen bunkasa musanya kasuwanci da tattalin arziki.
Mista Adesina ya kara da cewa, shugaba Buhari zai kuma yi shawarwari tare da shugabannin kasashen Larabawa domin sake duba yarjejeniyoyin da aka aiwatar domin karfafa huldar dangantaka dake fifita ci gaban noma da ababen more rayuwa a Najeriya, ta hanyar samun rancen kudi bisa tsawon lokaci da kuma musanyar kwarewar kimiyya da fasaha. (Maman Ada)