in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 14 suka mutu ko wace rana a tekun Mediterranean a bana
2016-12-28 13:15:45 cri

A kalla mutane 14 ne ke mutuwa a ko wace rana a kokarin tsallaka tekun Mediterranean a shekarar 2016, wannan shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu, kamar yadda mai magana da yawun ofishin MDD ya tabbatar da hakan a jiya Talata.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta ce, adadin mutanen da suka gamu da ajalinsu a tekun na Mediterranean a shekarar 2016 ya kai 5,000.

UNHCR ya bukaci kasashen duniya da su ba da daukin gaggawa domin magance matsalar, musamman ta hanyar baiwa 'yan gudun hijira mafaka, da baiwa iyalai baki izinin zama, da samar da guraben karatu ga dalibai.

A shekarar 2015, sama da mutane miliyan guda ne suka tsallaka tekun Mediterranean, kuma an samu hasarar rayukan mutane kimanin 3771.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China