Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD wato UNHCR, ta ce ta maida 'yan kasar Somaliya su kimanin 5,853 zuwa kasar su ta haihuwa, bayan sun shafe tsahon lokaci a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab dake arewacin kasar Kenya.
Ofishin hukumar ta UNHCR ya ce, a watan Nuwambar da ya shude, wasu 'yan gudun hijirar su 448 sun isa filin jirgin saman birnin Mogadishu. Bisa jimilla, daga watan Disambar bara ya zuwa wannan lokaci, an maida 'yan gudun hijirar 5,853 zuwa Somaliya.
A daya bangaren kuma hukumar ta ce, an dakatar da amfani da hanyoyin mota wajen maida 'yan gudun hijirar gida a lokacin damuna, saboda rashin kyawun hanyoyi.
Rahotanni na cewa, ana maida 'yan gudun hijirar ne yankunan Kismayu da Baidoa dake kudancin Somaliya, yankunan da a yanzu ke cikin kyakkyawan yanayin tsaro. A yanzu haka UNHCRn za ta ci gaba da wannan aiki har ya zuwa mako na 3 na watan Disambar nan.
Bisa kiyasi, yawan 'yan gudun hijirar Somaliya a Kenya sun kai sama da mutane 500,000, inda a sansanin Dadaab kadai yawansu ya kai mutane 350,000, wanda hakan ya sanya sansanin zamowa na daya a duniya wajen yawan 'yan gudun hijira.
Kimanin shekaru 20 ke nan 'yan kasar Somaliya ke samun mafaka a Kenya, a sakamakon tashe-tashen hankula dake addabar kasarsu. (Saminu)