in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR za ta fadada ba da tallafin kudi nan da 2020
2016-11-01 10:42:14 cri

Hukumar MDD mai lura da 'yan gudun hijira UNHCR, ta alkawarta fadada tallafin kudi da take baiwa masu gudun hijira a sansanonin kasashen daban daban nan da shekara ta 2020, a wani mataki na inganta rayuwa da ba da kariya ga 'yan gudun hijirar.

Da yake karin haske game da hakan cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, babban kwamishinan hukumar Filippo Grandi, ya ce sun lura da yadda tallafin kudade ke zama sanadiyyar inganta rayuwar wadanda tashe tashen hankula suka raba da gidajen su. Mr. Grandi ya ce, irin wadannan kudade da ake raba musu, na ba su damar biyan bukatun yau da kullum, tare da samar musu da damar bude sana'o'i mafiya dacewa su.

Kaza lika nasarwar ta ce, ba da tallafin kudi kai tsaye ga 'yan gudun hijira, na samar da yanayi na jituwa tsakanin su da al'ummun dake karbar bakuncin su.

Wani binciken baya bayan nan da jami'ar California, da hadin gwiwar cibiyar Davis, da shirin samar da abinci na MDD suka gudanar, ya gano cewa, tallafin kudade da ake bayarwa ga 'yan gudun hijirar dake kasar Uganda, ya haifar da ci gaban tattalin arziki mai tarin yawa. Bisa hakan ne kuma hukumar ta UNHCR, ta sha alwashin kara yawan kudaden da take bayarwa a matsayin taimako, a wasu karin kasashe 15, baya ga kasashe 60 da tuni suka fara cin gajiyar tsarin.

Kasashen da ake fatan 'yan gudun hijirar dake samun mafaka a cikin su za su ci wannan gajiya sun hada da Nijar, da janhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Kenya, da Congo Barazabil. Sauran su ne kasashen Rwanda, da Somalia, da Sudan, da Habasha, da Uganda, da Afghanistan da kuma Iran.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China