in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gidauniyar yaki da talauci ta Sin ta ba da gudumawar kayan abinci ga wasu makarantun firamare a Habasha
2015-11-27 09:54:07 cri

Wata gidauniyar yaki da talauci ta kasar Sin ta bayar da gudummawar kayayyyakin abinci karo na biyu ga shirin ciyar da dalibai a makarantun Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.

Gidauniyar dai ta tattara kudaden da yawansu ya kai dala dubu 171 daga daidaikun Sinawa tun lokacin da aka kaddamar da ita a watan Mayun wannan shekara.

A jawabinsa yayin bikin mika kayayyyakin da ya gudana a daya daga cikin makarantun da suka ci gajiyar shirin, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin ilimi na kasar Habasha Haileselassie Fisseha, ya ce, shirin ya taimaka wajen inganta harkokin ilimin firamare a marakantun da ke birnin.

Gudummawa ta baya-bayan da gidauniyar ta ba da ita ce, ciyar da dalibai kyauta a makarantun primary guda biyar a yankin Gulelle da ke wajen birnin Addis Ababa, inda sama da dalibai 1,000 za su amfana baya ga wasu dalibai 2,000 da suka ci gajiyar shirin a watannin da suka gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China