in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen saman Habasha zai kara yawan jigila zuwa birnin Guangzhou na Sin
2016-09-06 09:58:46 cri

Kamfanin jiragen sama na kasar Habasha wato Ethiopian Airlines, zai kara yawan zirga zirgar jiragen sa zuwa birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin.

Kamfanin dai na da aniyar kara jirage uku a ko wane mako, tun daga ranar 8 ga watan Oktoba mai zuwa, kari kan sufurin fasinjojin da yake yi a baya. Bisa wannan aniya, jiragen kamfanin za su rika kai komo sau 11 a birnin cikin ko wane mako.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban kamfanin Tewolde GebreMariam, ya ce, suna farin ciki da samun damar kara yawan sufurin su a Guangzhou, wanda daya ne daga birane mafiya girma a kasar Sin, yayin da kamfanin su ya kasance mafi samun karbuwa ga fasinjojin kasar Sin, da nahiyar Afirka, da kuma na kasar Brazil.

Ya ce, wannan mataki zai taka muhimmiyar rawa wajen habaka tattalin arzikin al'ummun wadannan yankuna, zai kuma bunkasa musaya tsakanin al'ummun Sin da na nahiyar Afirka.

Mr. GebreMariam ya kara da cewa, yanzu haka kamfanin Ethiopian Airlines na jigilar fasinjoji sau 31 a ko wane mako, tsakanin biranen Beijing, da Shanghai, da Guangzhou da kuma Hong Kong.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China