Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya fada cewar, talauci na daga cikin dalilan dake haddasa nuna wariya yayin mu'amala a cikin al'umma, inda ya yi kira da a dauki matakan dakile rashin daidaito a tsakanin al'umma ta hanyar yaki da fatara a tsakanin jama'a.
A sakon da ya aike na bikin tunawa da ranar yaki da talauci ta duniya, Ban ya ce, nuna kyama, da wariya, na daga cikin abubuwan dake haifar da rashin jituwa, da tsattsauran ra'ayi, da kuma tashe tashen hankulla da ake fama da su a sassan duniya dabam dabam.
Wata kididdiga da MDD ta fitar ta nuna cewa, a halin yanzu sama da mutane biliyan daya ne ke fama da matsanancin talauci, sannan wasu miliyan 800 na fama da yunwa da karancin abinci a fadin duniya.
Ban ya ce, dole ne a gina al'umma bisa tsarin da kowa zai shiga a dama da shi.
Ana gudanar da bikin tunawa da ranar yaki da fatara ne a ranar 17 ga watan Oktoba na kowace shekara, domin wayar da kan al'umma game da muhimmancin yaki da matsanancin talauci a dukkannin kasashen duniya.
Taken bikin na wannan shekara shi ne, "sauyawa daga nuna wariya da kyama zuwa kowa ya shiga a dama da shi: kawar da dukkannin nau'ikan talauci".(Ahmad Fagam)