A karon farko, kasar Ghana ta ba da damar girke na'urorin talabijin a cibiyoyin tattara sakamakon zaben kasar da za'a gudanar a watan Disamba domin a kalli yadda ake tattara sakamakon zaben kai tsaye ta gidaden talabijin din kasar.
Kafafen yada labaran kasar sun jiyo shugabar hukumar zaben kasar Charlotte Osei, tana bayyana hakan a jiya Alhamis.
Osei, wacce ta bayyana hakan a wani taron dandalin editoci da aka gudanar a Accra, ta ce wannan mataki zai ba da damar samun zabe mai inganci a zabukan shugaban kasa, da na majalisar dokokin kasar da za'a gudanar a ranar 7 ga watan Disamba.(Ahmad Fagam)