in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta ce an kashe jakadanta domin hana wanzar da zaman lafiya a Syria
2016-12-21 09:38:03 cri

A daren ranar Litinin ne, wani 'dan bindiga ya harbe jakadan kasar Rasha dake kasar Turkiya Andrey Karlov har lahira yayin da yake halartar wani bikin nune-nunen zane-zane mai taken "Yadda al'ummar Turkiya ke kallon Rasha" wanda aka shirya a birnin Ankara, fadar mulkin kasar ta Turkiya. Rahotanni na cewa, wani 'dan sandan Turkiya sanya da kayan mai gadi ya harbe jakadan na kasar Rasha, inda nan take shi ma aka kashe shi. Yanzu dai ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta mayar batun tamkar harin ta'addanci ne.

Jiya Talata shugaban majalisar wakilai ta Rasha wato Duma Vyacheslav Volodin ya bayyana cewa, makasudin kashe jakadan Rasha dake Turkiya shi ne domin hana cimma yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Syria, a don haka ya ce, ya zama wajibi kasashen duniya su kara zage damtse domin warware rikicin da Syria ke fuskanta.

Shugaban Rasha Vladimir Putin shi ma ya bayyana cewa, harin ta'addancin da aka kai wa jakadan kasarsa ya jefa al'ummar kasar cikin zaman zullumi, kuma yanzu ana gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, bangarorin biyu wato Rasha da Turkiya ba za su daina hadin gwiwa a tsakaninsu kan batun Syria ba, kana kwamitin binciken da aka kafa cikin hadin gwiwar sassan biyu domin gudanar da bincike kan kisan ya riga ya fara aiki.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China