in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta bayyana musabbabin rasuwar matukan jirginta da aka kakkabo
2015-11-25 09:51:22 cri

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta ce, binciken farko da aka gudanar, ya nuna cewa, daya daga cikin matuka jirgin saman yakinta da aka kakkabo ya rasu ne sakamakon wuta da ta kama lemar da ya yi yunkurin sauka da ita daga jirgin, yayin da dayan kuma ya rasa ransa lokacin da ake kokarin ceton sa.

A ranar Talata ne dai dakarun kasar Turkiya suka harbor jirgin saman yakin na Rasha, bayan da suka yi wa matukan jirgin gargadi game da keta sararin saman Turkiya ba tare da izini ba, ko da yake Rasha ta ce, an harbor jirgin nata ne a sararin saman kasar Syria.

Kalaman na rundunar tsaron kasar Rasha dai sun sabawa na dakarun Turkiya, inda sojojinta suka ce sai da suka gargadi jirgin Rashan har sau 10 kafin su harbo shi. Tuni Rasha ta bayyana bacin ranta game da harbo jirgin. A cewar mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar ta Rasha Sergei Rutskoy, za a dakatar da musayar sakwanni tsakanin rundunonin sojojin kasashen biyu. Kaza lika Rasha za ta tsaurara matakan tsaro a sansanin jiragen samanta dake kasar Syria, tare da tabbatar da kariya ga jiragen yakinta.

A daya bangaren kuma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, akwai sakamako da zai biyo bayan wannan al'amari da ya auku.

A wani ci gaban kuma sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya yi kira ga sassan biyu da su kai zuciya nesa. Mr. Stoltenberg ya bayyana hakan ne bayan wani taron gaggawa da wakilan kungiyar ta NATO suka gudanar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China