in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO na goyon bayan Tanzaniya domin kara noman shinkafa
2016-11-15 11:14:37 cri

Kasar Tanzaniya da hukumar noma da abinci ta MDD (FAO) sun cimma wata yarjejeniyar hadin gwiwa a ranar Litinin, yarjejeniyar da za ta taimakawa kasar dake gabashin Afrika kara ninka noman shimkafarta har sau biyu nan da shekarar 2018.

Wannan sabuwar yarjejeniya da aka yiwa taken "hadin gwiwa domin bunkasa noman shimkafa a Afrika cikin karko," an kaddamar da ita a yankin Morogoro, mai tazarar kilomita 200 daga yammacin babban birnin tattalin arzikin kasar wato Dar es Salaam.

Fred Kafeero, wakilin hukumar FAO dake Tanzaniya, ya bayyana cewa, wannan sabon shiri na dalar Amurka miliyan biyar na da burin tallafawa kokarin Tanzaniya domin ninka noman shimkafarta har sau biyu nan da shekarar 2018 ta hanyar karfafa samar da albarkatun noma ga manoman kasar.

Irin wadannan ayyukan, ana gudanar da su a yanzu haka a cikin kasashen Afrika goma, da suka hada da ita Tanzaniyar, Kenya, Uganda, Cote d'Ivoire, Najeriya, Guinea, Mali, Benin, Kamaru da Senegal. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China