in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO da Mali sun kaddamar da shirin maido da tsaron abinci a arewacin kasar
2015-04-02 14:21:32 cri

Gwamnatin kasar Mali da kungiyar abinci ta duniya (FAO) sun kaddamar a ranar Laraba da aiwatar da ayyukan wani shiri na dalar Amurka miliyan biyar domin maido da hanyoyin samar da abinci a wuraren dake fama karancin abinci sakamakon tashe tashen hankali na baya baya da na matsalar sauyin yanayi a arewacin kasar.

Sanarwar ta fito daga ministan ci gaban karkara na kasar Mali, Bokary Treta, da kuma babban darektan kungiyar FAO, Jose Graziano da Silva, dake ziyarar aiki a kasar.

Ayyukan wannan shirin dai za su taimaka wajen ingiza samar da abinci ga mutane dubu 25 dake cikin mawuyacin hali, tare da tallafawa iyalai makiyaya dubu 8 masu karamin karfi ta hanyar ba su abinci da kayayyakin kula da lafiyar dabbobinsu.

Haka zalika, shirin zai samar da wata damar ba da horo bisa aikin noma na gari, da samar da abinci mai gina jiki ga iyalan da suka samu wannan gajiya, tare da ba da muhimmanci ga kungiyoyin mata dake aikin samar da kayan lambu.

Wannan shiri na bisa tsarin ingiza da sake gina tattalin arziki na bankin duniya a kasar Mali da ya kai dalar Amurka miliyan 100. Haka kuma bisa bukatar gwamnatin kasar Mali, kungiyar FAO za ta daukar nauyin aiwatar da bangaren sha'anin noma a arewacin kasar Mali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China