A kalla mutane 69 ne suka rasa rayukan su, kana wasu 55 suka samu raunuka, yayin da wasu mahara suka aukawa kauyukan Dalori da Walori, dake kusa da birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Bornon Najeriya.
Rahotanni sun ce wasu mahara ne suka kaddamar da hare-haren na ranar Asabar, ciki hadda mata 'yan kunar bakin wake su uku, wadanda suka tada bama-baman dake jikin su, bayan da suka kutsa kai cikin taron jama'a.
Wata majiyar jami'an lafiya daga birnin Maiduguri, ta ce jami'an 'yan sanda, da na kungiyar Red Cross, tare da na hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ne, suka kai gawawwakin wadanda suka rasu da masu raunuka zuwa babban asibitin birnin.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kakakin rundunar yaki da ayyukan ta'addanci a Najeriyar Kanar Mustapha Ankas, ya ce maharan sun yi amfani da bindigogi da ababen fashewa wajen kaddamar da hare-haren kan fararen hula a kauyukan biyu. Kaza lika sun cinnawa gidade da dama wuta.
Har wa yau maharan sun yi yunkurin aukawa sansanin 'yan gudun hijira dake makwaftaka da yankin, lamarin da ya haddasa musayar wuta, da fashewar bama bamai, kafin kuma sojoji su tilasawa maharan janyewa.(Saminu)