in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan bindiga sun kai hari a yankin arewa maso gabashin Najeriya
2016-01-25 09:38:52 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu 'yan bindiga sun halaka mutane da dama, a wani hari da suka kaddamar a kauyuka da ke yankin Girei a jihar Adamawa da ke shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Othman Abubakar ya tabbatar da aukuwar harin na jiya Lahadi. Wanda ya rutsa da jami'in 'yan sandan yankin Vunokilang

Maharan dai sun fara kaddamar da hare-hare a kauyukan hudu ne da misalin karfe 5.30 na asubahi, agogon wurin, inda suka halaka mutane da dama, sannan suka bankawa gidaje wuta.

Mai rikon mukamin kwamandan birget ta 23 da ke birnin Yolan jihar Adamawa Kanar Aba Poopola ya bayyana cewa, an tura sojoji zuwa kauyukan da harin ya shafa da nufin shawo kan lamarin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China