in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar da Rasha na fatan kara karfafa dangantakarsu
2016-10-13 09:55:40 cri

Kasashen Nijar da Rasha sun dauki niyyar sake karfafa dadaddar dangantakarsu ta fiye da tsawon shekaru 40 ta hanyar daddale wata yarjejeniya a ranar Talata a birnin Yamai tsakanin ministan harkokin waje da dangantaka na Nijar, Ibrahim Yacouba, da mataimakin ministan harkokin wajen Rasha, Milkhail Bogdanov, wanda shi ma manzon musamman ne na shugaban Rasha.

Yarjejeniyar za ta baiwa Rasha da Nijar damar kara zurfafa dangantakarsu ta fuskar tsaro da ci gaba. Bisa wannan yarjejeniyar, ma'aikatun namu biyu za su rika gudanar da shawarwari kan batutuwa masu muhimmanci ga kasashen namu biyu, har ma da batutuwan kasa da kasa, in ji mista Yacouba.

Haka kuma ya nuna cewa, Nijar za ta yi aiki domin kafa tare da Rasha wata dangantakar da za ta tallafa ci gaban kasarsa.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Milkhail Bogdanov ya jaddada cewa, yarjejeniyar za ta samar da wani sabon yunkuri ga dangantakar Rasha da Nijar, kasarsa a shirya take domin yin aiki tare da Nijar.

Kafin da aka daddale yarjejeniyar, manzon musammun na shugaba Putin Milkhail Bogdanov ya samu ganawa tare da shugaban Nijar Mahamadou Issoufou, inda shugaban Nijar ya bayyana niyyarsa ta bunkasa dangantaka a fannin tsaro da ci gaba tsakanin kasashen biyu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China