in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar za ta yi atisayen soji da Rasha a makon gobe
2016-10-13 10:24:23 cri

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Masar ya ce, a mako mai zuwa ne kasar za ta karbi bakuncin atisayen soji na hadin gwiwa da kasar Rasha wanda aka yiwa taken "abotar masu ba da kariya ta 2016".

Kakakin sojin na Masar ya kara da cewa, atisayen soji na Masar da Rasha, wani bangare ne na shirin horas da sojoji na rundunar sojin kasar Masar, a cewarsa, kasar Masar tana gudanar da horon sojoji na hadin gwiwa da kasashen duniya sama da 30, kuma tana gudanar da shirin a kalla sau 20 a duk shekara.

Dangantaka tsakanin Masar da Rasha na ci gaba da bunkasa ne, tun lokacin da shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya dare karagar mulkin kasar a shekarar 2014, duk kuwa da hadarin da jirgin saman Rashan ya yi a yankin Sinai na kasar Masar a bara wanda ya lakume rayukan mutane sama da 200, kuma mafi yawan wadanda suka mutu 'yan kasar Rasha ne.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China