in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana shirye-shiryen gudanar da taron zaman lafiya game da Syria a Geneva
2016-01-14 10:04:35 cri

Manzon musamman na MDD mai kula da batun Syria, Staffan de Mistura ya bayyana kudirinsa na ganin ya gayyacin dukkan sassan masu ruwa da tsaki a rikicin kasar Syria a tattaunawar sulhun da za a yi game da Syrian a birnin Geneva.

Jami'in na MDD ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da wakilan kwamitin sulhu na MDD wato kasashen Amurka, Rasha, Faransa, Burtaniya da kuma Sin. Inda ya yi musu karin haske game da sakamakon ziyararsa ta baya-bayan nan da ya kai shiyyar da kuma shirye-shiryen da ake game da tattaunawar ta Genava.

Sai dai galibin kungiyoyin 'yan adawar kasar ta Syria sun ce ba za su halarci taron zaman lafiyar da za a yi a Genava ba, har sai an aiwatar da kudurin jin kai da MDD ta gabatar, wadda ke kira ga sassan da ke gwabza fada da juna da su ba da damar kai kayan agaji ga fararen hula da ke matukar karancin abinci.

Tun da farko ministan harkokin wajen kasar Syria Walid al-Moallem ya bukaci a gabatar da sunayen kungiyoyin adawar da za su halarci taron ta Genava da tsagin gwamnatin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China