in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana neman wasu mayakan Boko Haram 55 ruwa a jallo
2016-11-22 09:24:46 cri

A jiya Litinin Najeriya ta ayyana sunaye tare da hotunan mayakan Boko Haram da take nema ruwa a jallo, sakamakon zarginsu da hannu wajen kaddamar da hare haren ta'addanci a yankin arewa maso gabashin kasar, inda jami'an sojin kasar ke ci gaba da fafatawa da 'yan tada kayar bayan.

Babban jami'i a hukumar tsaron kasar Janar Abayomi Gabriel Olonishakin, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ayyana neman 'yan ta'addan, kana ya bukaci al'umma da su taimaka wajen zakulo mutanen.

Jami'in sojin ya bukaci mayakan na Boko Haram dake da sha'awar mika wuya da su hanzarta yin hakan, domin shiga shirin yafiya ga tubabbun 'yan Boko Haram karkashin shiri na rundunar sojin kasar.

A nasa bangaren, babban hafsan sojojin kasa na Najeriyar Laftanal janar Tukur Buratai, ya ce rundunar sojin kasar ta fitar da sunayen farko na mayakan Boko Haram da take nema a karshen shekarar 2015 ne, ya kara da cewa, wannan shi ne karo na biyu da rundunar sojin ta ayyana sunayen mayakan da take nemansu ruwa a jallo.

Ya ce, sabon jerin sunayen na baya bayan nan da rundunar ta fitar, ya hada har da suna da kuma hoton kwamandan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, kuma wannan shi ne karo na 3 da rundunar da ayyana neman mayakan a bainar jama'a.

A cewarsa, rundunar sojin kasar ta dauki wannan mataki na ayyana sunayen ne da nufin jaddada muhimmancin neman da take yiwa mayakan, sannan ta bukaci jama'a da su taimakawa hukumomi da muhimman bayanai game da mayakan na Boko Haram.

Da yake tsokaci game da yakin da dakarun kasar suke yi da 'yan ta'adda, Buratai ya nanata cewa, sojojin Najeriyar sun karya lagon Boko Haram, kuma babu shakku a game da haka.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China