Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi kiran da a rika sanya manufofi da akidu cikin abubuwan da ake koyarwa a kwalejojin kasar, a wani mataki na samun cikakken jagorancin jam'iyya a manyan makarantu.
Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS kana shugaban rundunar sojojin kasar, ya bayyana hakan ne yayin taron kwanaki biyu game da ayyukan da suka shafi akidu da harkokin siyasa a kwalejoji da jami'oin kasar Sin da aka kammala a yau Alhamis. (Ibrahim)