in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ba za ta nuna sassauci ba game da tashe tashen hankalin zabuka
2016-10-26 10:33:47 cri

Jiya Talata ministan dake kula tsaron cikin gidan Ghana, Prosper Douglas Bani, ya bayyana matakin kin rufe ido game da tashe tashen hankalin zabuka a cikin tsarin gudanar da zabukan gama gari a cikin wannan kasa.

Da yake magana gaban 'yan jarida a birnin Accra, mista Bani ya yi kashedi ga masu niyyar tada kayar baya domin gurbata zabuka da su fasa daga wannan aiki, domin jami'an tsaro ba za su rufe ido ba kan duk wata hatsaniya ba, a lokacin zabuka da kuma bayan zabuka.

Ba za mu nuna hakuri ko guda ba ga duk wani mutumin ko gungun mutane dake fatan gurbata zaman lafiya. 'Yan sanda za su mayar da martani cikin gaggawa, kuma za a gurfanar da duk masu hannu gaban kuliya cikin lokaci, in ji mista Bani.

Yan kasar ta Ghana za su jefa kuri'u a ranar 7 ga watan Disamba domin zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisu 275.

Duk da cewa fiye da 'yan kwanaki arba'in suka rage kafin zabukan, ma'aikatar 'yan sandan Ghana ta bayyana cewa, ta tantance wurare fiye da dubu biyar domin kaucewa tashe tashen hankali.

Mista Bani ya yi kira ga 'yan Ghana da su karfafa kokarin jami'an tsaron kasar domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Ghana.

Za mu ci gaba cikin ko ta kwana da sanya ido kan zaman lafiya da muke fata, in ji mista Bani.

Yan takara hudu ne suka sami iznin shiga takarar zaben shugaban kasar ta Ghana daga babbar hukumar zabe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China