in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 5 sun mutu a harin igwa mai luguden wuta a Mogadishu
2016-02-26 09:20:47 cri

A kalla mutane 5 ne aka tabbatar da mutuwar su, yayin da wasu mutane 7 suka jikkata bayan wani harin da aka kaddamar da igwa mai luguden wuta a kusa da fadar shugaban kasar Somaliya a ranar Alhamis da ta gabata.

Abdikshakur Ismail, jami'in 'yan sanda ne dake aiki a fadar shugaban kasar ya bayyana cewar, har yanzu ba'a gano ainihin daga inda wannan igwa ta fito ba, kuma nan take harin ya hallaka mutane 5 dake kusa da wurin.

Shedun gani da ido sun bayyana cewa, sun ji karar fashewar wasu abubuwa daga lokacin da igwar ta isa wajen.

Mai magana da yawun hukumar gudanarwar lardin Benadir Abdiftah Omar Halane, ya tabbatar da mutuwar mutanen biyar, kuma ana kyautata zaton mutanen da harin ya rutsa da su iyali guda ne da kuma wani malamin addinin Islama.

Tuni dai kungiyar Al-shabaab dake yin biyayya ga Al-Qaida ta dauki alhakin kaddamar da harin a Mogadishu, kungiyar ta ce, ta girke makamai masu linzami guda 9 a kusa da fadar shugaban kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China