A ranar 22 ga wata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta fidda wata sanarwa, wadda ke cewa sojojin Amurka sun kai hari ta sama, a yankunan kudu maso yammacin kasar dake da iyaka da kasar Afghanistan, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 2, sai dai cikin sanarwar, ba a fayyace ko akwai jagoran kungiyar Taliban Akhtar Mohammad Mansour cikin wadanda harin ya rutsa da su ba.
A baya Mansour shi ne mataimakin tsohon jagoran kungiyar Taliban Mullah Mohammad Omar, kuma a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2015, ya zama sabon jagoran kungiyar don maye gurbin Omar, wanda ya rasu sakamakon wata rashin lafiya.(Bako)