in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyya mai mulki a Ghana ta fidda manufofinta gabannin fara yakin neman zabe
2016-09-19 09:23:56 cri

Jam'iyyar NDC mai mulki a Ghana, ta fidda manufofin ta na ciyar da kasa gaba, gabannin fara yakin neman zaben kasar.

Shugaba Dramani Mahama wanda ya jagoranci gangamin fidda akidun jam'iyyar a Sunyani, fadar mulkin Brong Ahafo, wanda ke da nisan kilomita 400 arewa da fadar mulkin kasar, ya ce, kundin jam'iyyar da aka yiwa lakabi da "hanyar sauya rayuka, don kawo sauyi ga kasar Ghana" na kunshe da dabarun sauya alkiblar kasar cikin shekaru 4 masu zuwa.

Shugaba Mahama ya ce, sun shirya tsaf, don ganin sun ciyar da tsarin ilimi da lafiya, da zamantakewar al'ummar kasar ta Ghana gaba. Ya ce, hakan wata dama ce ta fadada ikon 'yan kasar na samun ayyukan yi, tare da bude kofofin sana'o'i ga matasa.

Har wa yau shugaban na Ghana ya lasafta fannonin karfafa tattalin arziki, da na samar da ababen more rayuwar jama'a, tare da gudanar da gwamnati a bude, a matsayin manyan ginshikan akidun jam'iyyar ta NDC mai mulki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China