in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Senegal na fargabar dawowar matasa masu jahadi da suka tafi Libya da Syria
2016-12-08 10:40:01 cri

Hukukomin siyasa da na sojojin kasar Senegal sun bayyana fargabarsu kan dawowa gida na matasan kasar masu jahadi da suka tafi Libya, Najeriya ko Syria a yayin dandalin Dakar kan zaman lafiya da tsaro karo na uku.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya yi tsokaci kan wasu 'yan kasar masu takardar shaidar 'yan kasa biyu da suka tashi daga Dakar zuwa sansanonin kungiyar IS dake Syria. Shugaban Senegal din ya goyi bayan yaki ba kakkautawa, tare da ba da shawarar kadda a yi kasa a gwiwa wajen wannan yaki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China