in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Senegal ya isa Bamako domin nuna goyon bayansa bayan hari a Mali
2015-11-23 10:02:06 cri

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya isa birnin Bamako a ranar jiya Lahadi domin nuna goyon bayan al'ummar Senegal ga 'yan uwansu na Mali. A filin jirgin saman kasa da kasa na Senou dake Bamako, shugaba Macky Sall da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita sun isa wajen girmama gawar 'dan kasar Senegal da aka kashe a ranar Jumma'ar da ta gabata a lokacin wani harin ta'addancin da aka kai a ginin otel din Radisson Blu dake Bamako, in ji wani mai ba da shawara ta fuskar sadarwa a fadar shugaban kasar Mali.

Harin ta'addancin otel Radisson Blu, wanda ya biyo tare da yin garkuwa da mutane, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21 da jikkara 17, a cewar wani adadin karshe da ministan tsaron Mali manjo kanal Salif Traore ya bayar a ranar Asabar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China