in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Senegal ta gudanar da taro kan inganta harkokin kasar
2016-05-31 09:26:27 cri

A karshen makon da ya gabata ne shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya kaddamar da wani taro kan yadda za a saita alkiblar kasar.

Manufar taron wanda ya hallara kan wakilai daga bangarorin jam'iyyun siyasu, kungiyoyin fararen hula, kwadago, addinai, da sarakunan gargajiyar kasar da sauransu, ita ce, lalubo bakin zaren, yadda za a aiwatar da gyare-gyaren da aka cimma a kundin tsarin mulkin kasar a lokacin kuri'ar jin ra'ayin jama'ar kasar da ta gudana a ranar 20 ga watan Maris.

Bugu da kari, mahalarta taron sun tattauna batutuwan da suka shafi harkokin tsaro, daukar nauyin jam'iyyun siyasu da kuma dokokin zabe.

A jawabinsa, shugaba Sall ya bayyana kudurinsa na cimma matsaya da masu ruwa da tsaki a bangarorin kiwon lafiya da ilimi wadanda suka sha fuskantar yajin aiki a 'yan kwanakin nan.

Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki a bangaren sassa masu zaman kansu, da su kara ba da gudummawa a kokarin da ake yi na raya tattalin arzikin kasar, da samar da guraben aikin yi don ganin an magance matsalar aikin yi da ake fama da ita a kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China