in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci a dauki karin matakan warware rikicin DRC ta hanyar tattaunawar siyasa
2016-12-06 10:16:20 cri

Kasar Sin ta bukaci kasashen duniya da su dauki kwararan matakan tattaunawa ta hanyar siyasa domin samar da dauwamamman zaman lafiya mai dorewa a jamhuriyar demakaradiyyar Congo DRC.

Wu Haitao, shi ne mataimakin wakilin din din din na kasar Sin a MDD, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron kwamitin tsaron MDD game da halin da ake ciki kan rikicin DRC.

Wu ya ce, tattaunawar siyasa ce kadai mafita, wajen warware dambarwar siyasar kasar Congo. Ya kara da cewa, shugaba Joseph Kabila da gwamnatin jamhuriyar demokaradiyyar Congo a shirye suke su shiga tattaunawar sulhu don kawo karshen rikicin kasar, ta yadda za a samu kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki a kasar, wanda kuma kasar Sin ta yi na'am da wannan matsayi.

Domin daukar wannan mataki na warware rikicin a DRC ta hanyar siyasa, mista Wu ya ce, gwamnatin DRC da kungiyoyin 'yan tawaye masu ruwa da tsaki a rikicin kasar, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar shirya zabe, da kafa gwamnatin hadin kan kasa, da kuma zaben wanda zai rike mukamin firaiministan kasar.

Ya ce, dama dai kasar Sin ta aike da dakarun wanzar da zaman lafiya ga tawagar MDD a DRC.

Kuma kasar Sin a shirye take ta ci gaba da goyon bayan matakan da za su tabbatar da samun dauwamamman zaman lafiya a DRC, in ji Wu Haitao.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China