in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ci galabar dakile annobar zazzabin shawara a Angola da DRC
2016-09-14 10:59:46 cri

Kwararru a hukumar lafiya ta duniya WHO sun bayyana cewa, an samu nasarar shawo kan annobar zazzabin shawara wato yellow fever da ta barke a kasashen Angola da jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC, sakamakon gangamin allurar riga kafin cutar da aka gudanar a kasashen biyu.

Sylvie Briand, daraktan kula da kwayoyin cutuka na hukumar WHO ya bayyana a taron manema labarai game da dabarun da hukumar lafiya ta duniyar ke dauka wajen dakile yaduwar cutar, ya ce, a halin yanzu an shawo kan wannan annoba, kuma ba'a samu rahoton wanda ya sake kamuwa da cutar a kasar Angola ba tun a ranar 23 ga watan Yuni, a DRC ma ba'a samu ba tun a ranar 12 ga watan Yulin.

A 'yan kwanakin nan, an gudanar da gangamin alluran rigakafin cutar ne da nufin dakile yaduwar kwayoyin cutar, to sai dai babban abin da ake fargaba shi ne, yadda za'a hana kwayoyin cutar sake bazuwa a nan gaba, musamman a lokacin farkon damina.

Briand ya ce, barazanar barkewar cutar ya karu a kwanakin baya, sakamakon yawaitar tafiye tafiye da ake samu na al'ummomi a tsakanin kasashen Afrika, musamman daga kasashen da ake fama da cutar, har ma da sauran kasashen duniya inda ake fuskantar bala'o'i da rikice rikice.

Bugu da kari, matsalar karuwar sauyawar yanayi ta El Nino, wanda ke haddasa ruwan sama, lamarin da ke janyo karuwar sauro musamman a yankunan birane, shi ma na daga cikin barazanar game da yaduwar cutar zazzabin shawarar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China