in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taliban a Pakistan ta dauki alhakin kai harin filin jirgin Karachi
2014-06-09 14:47:13 cri

Kungiyar Taliban a kasar Pakistan ta ce, ita ce ta kaddamar da harin nan da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 19, tare da jikkata wasu 23 a filin tashi da saukar jiragen sama dake Karachi, a daren ranar Lahadin da ta gabata.

A cewar kakakin dakarun kungiyar ta TTP Shahidullah Shahid, sun kaiwa filin jirgin na Jinnah hari ne, a matsayin ramuwar gayyar kisan tsohon jagoran su Hakeemullah Mehsud, wanda wani jirgin yakin Amurka ya hallaka cikin watan Nuwambar bara.

Tuni dai rundunar sojin kasar ta Pakistan ta bayyana cewa, dukkanin 'yan bindigar da suka kai hari filin jirgin su 10 sun rasa rayukan su, yayin musayar wuta da ta auku tsakanin su da jami'an tsaro.

Kafofin yada labarun kasar dai sun ce, tun da fari 'yan bindigar sun kutsa filin jirgin saman na Jinnah ne, ta sashin da ake ajiye jiragen dakon kaya, suka kuma budewa jami'an tsaron dake sashen wuta, kafin daga bisani su kunnawa wasu jiragen kasashen ketare biyu wuta.

Jami'an tsaron kasar dai na ci gaba da gudanar da bincike game da aukuwar harin, yayin da kuma a hannu guda firaministan kasar Mawaz Sharif ya kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike na musamman, ya kuma mika sakamakonsa ga mahukuntan kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China