in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na da imanin shiga cikin kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya
2015-03-20 10:50:30 cri

Kasar Najeriya ta bayyana fatanta na kasancewa daya daga cikin kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya, ta hanyar aiwatar da wata manufar kasa mai inganci (National Quality Policy) wato NQP, in ji ministan kasuwancin Najeriya Olusegun Aganga a ranar Alhamis.

Wannan kundi ne da 'yan Najeriya suka tsara domin kuma 'yan Najeriya da zummar cimma burin guda na daidaita matsayin Najeriya cikin kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya a cikin lokaci, in ji mista Aganga a lokacin da ya karbar kofin wannan kundi a birnin Abuja, hedkwatar kasar.

NQP na da manufar bullo da wani tsarin da ya dace domin bunkasa da fitar da ka'idojin kasa.

Ministan ya bayyana cewa, kundin NQP na kasance wani tushen tsari na daidaita tsaro domin taimakawa Najeriya wajen bunkasa kirkirowa, kimiyya, masana'antu, samar da ayyukan masu inganci da zaman rayuwa mai kyau. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China