in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ba da babbar gudummawa wajen karuwar tattalin arzikin Asiya da tekun Pasific, in ji rahoton MDD
2016-12-02 10:28:52 cri

Jiya Alhamis ne, kwamitin kula da tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasashen da ke Asiya da tekun Pasific na MDD wato ESCAP ya bayar da wani rahoto kan halin da kasashen Asiya da na tekun Pasific ke ciki a fannonin tattalin aziki da zaman al'umma a shekarar 2016, inda ya bayyana cewa, ko da yake ana samun tabarbarewar tattalin arzikin duniya, da rashin karfin karuwar yawan cinikayyar duniya, gami da rashin sanin tabbas kan makomar karuwar tattalin arzikin muhimman kasashe masu ci gaba a halin yanzu, amma tattalin arziki na kasashen Asiya da na tekun Pasific yana ta samun saurin karuwar ba tare da wata tangarda ba bisa babbar gudummawar da kasar Sin ta bayar a wannan fanni, wanda ya kasance wani abun dogara da ci gaban tattalin arzikin duniya.

Rahoton na nuna cewa, yawan karuwar tattalin arzikin kasashe masu tasowa da ke Asiya da tekun Pasific zai kai kashi 4.9 cikin kashi dari a shekarar 2016, wanda yake a sahun gaba a duk fadin duniya. A waje daya kuma, rahoton ya daidaita hasashen da ya yi wa yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2016 da ta 2017, wato a ganinsa, yawan GDP da kasar Sin za ta samu zai kai 6.7% da 6.4% a wadannan shekaru biyu.

Bugu da kari, rahoton ya yi hasashen cewa, a 'yan shekaru masu zuwa, tattalin arzikin kasar Sin zai kara samun bunkasuwa yadda ya kamata, kuma kasar Sin za ta iya cimma burinta da aka gabatar cikin shiri na 13 na shekaru 5 na raya kasar. Haka zalika, rahoton na ganin cewa, shirin "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar ya dace da yanayin musamman na yankin Asiya da na tekun Pasific, wanda zai ba da taimako sosai wajen farfado da tattalin arzikin yankin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China