in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da a yi kokarin kawo karshen cutar kanjamau
2016-12-02 10:05:16 cri

Jiya Alhamis babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da wani jawabi game da ranar yaki da cutar kanjamau, inda ya kirayi kasashen duniya da su gama kai domin kawo karshen cutar nan da shekarar 2030.

A cikin jawabinsa, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, an riga an samu babban sakamako a fannin rigakafi da kuma magance cutar kanjamau, adadin masu dauke da cutar wadanda ke samun jinya ya karu. Tun daga shekarar 2000, adadin yaran da suka kamu da cutar daga jikin mahaifansu ya ragu har da kashi 50 cikin dari, kana adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar shi ma ya ragu, kazalika, masu fama da cutar suna samun jinya yadda kamata.

Ban Ki-moon ya ci gaba da cewa, duk da cewa, an samu ci gaba, amma akwai matsala dake gabanmu, musamman ma a kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara, mata sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar, kuma da kyar ne mutanen dake fama da talauci suke samun hidima da kuma jinya.

Ban Ki-moon ya kara da cewa, ajandar MDD kan kawo karshen cutar kanjamau nan da shekarar 2030 ta yi alkawari cewa, za a cimma burin a ko wace kasa a fadin duniya, a saboda haka ya yi kira da a samar da taimako ga kowane mutumin da yake bukata.

Tun bayan da aka gano mutumin dake dauke da kwayoyin cutar kanjamau na farko a kasar Amurka a shekarar 1981, cikin sauri ne cutar ta yadu a fadin duniya. Bisa kididdigar da hukumar shirin cutar kanjamau ta MDD ta yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2015, gaba daya adadin mutanen wadanda suka dauke da kwayoyin cutar kanjamau a fadin duniya ya kai miliyan 36 da dubu 700, kana adadin mutanen da suka rasa rayuka bisa dalilin da ke da nasaba da cutar kanjamau ya kai miliyan 1 da dubu 100 a shekarar 2015 da ta gabata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China