Yanzu haka mazauna birnin Beijing da na Tianjin, da na lardin Hebei, da na Henan sama da miliyan 42 sun ci gajiyar wannan shirin. Ban da haka kuma,an ce dalilin wannan aiki ne ingancin ruwan sha ya samu kyautatuwa, yayin da aka samu damar sassanta yanayin raguwar yawan ruwa a karkashin kasa, har ma a wasu wuraren, yawan ruwan karkashin kasa ya fara karuwa. Bugu da kari, an kyautata muhallin halittu na koguna da tabkoki na wasu birane, tare da samun moriyar zaman al'umma da na tattalin arziki da kuma na halittu.(Fatima)