in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta bullo da sabon tsari da nufin daga darajar kudin kasar
2016-06-16 09:31:37 cri

Babban bankin Najeriya CBN, ya sanar da wasu sabbin ka'idoji na hada-hadar kudaden waje a kasar domin kare da kuma farfado da darajar Naira.

Ka'idojin sun hada da kafa sabuwar kasuwa ta musamman, wadda za ta rage bukatar kudaden kasashen waje da matsin lambar da kudin kasar ke fuskanta.

Zai kuma bai wa 'yan kasuwa tabbaci domin su san cewar za su samu kudade na kasashen waje da zarar sun bukata.

Gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin taron manema labaru a Abuja, fadar mulkin kasar.

Emefiele ya ce, sabon tsarin zai taimaka wajen cike gibin faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, wanda ya yi matukar haifar da koma baya ga tattalin arzikin na Najeriyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China