Hukumar bayar da taimakon agajin gaggawa ta Nigeriya ta baiwa 'yan gudun hijirar Nigeriya da suka fake a jamhuriyar Nijar taimakon kayayyakin agaji da suka kai tan 540 .
A cikin wata sanarwa da ta bayar, hukumar ta ce, an samar da kayayyakin agajin da suka hada da abinci da kuma kayayyakin masarufi ga dimbin 'yan Nigeriya da yanzu haka suke zaune a wurarre dabam-dabam a yankin Diffa na jamhuriyar Nijar.
Kididdiga ta nuna cewar, 'yan gudun hijirar wadanda yawancinsu sun fito ne daga jihohin Adamawa, Borno da Yobe dake arewa maso gabashin Nijeriya, sun tsallaka kasar Nijar a sakamakon zafin hare-haren mayakan kungiyar 'yan tada zaune tsaye ta Boko Haram.
Hukumar bayar da taimakon agajin gaggawa ta ce, gwamnatin Nigeriya za ta ci gaba da tuntubar gwamnatin Nijar domin tabbatar da cewar, dukanin 'yan gudun hijira na Nigeriya sun zauna cikin yanayi mai inganci domin tabbatar da cewar, an taimaka wa daukacin 'yan Nijeriya dake cikin kunci.
Sanarwar ta kara da cewar, Nigeriya ta jinjinawa gwamnatin Nijar saboda juriyar da ta nuna wajen baiwa 'yan gudun hijirar mafaka tare da daukar mataki na tsaron lafiyarsu.
Shi dai yankin na Diffa ya kai nisan kilomita 25 daga jihohin Yobe da Borno.
Hukumar bayar da agajin ta ce, har yanzu akwai sauran aiki domin tana da shirin bayar da taimakon agaji ga sauran 'yan gudun hijira na Nigeriya wadanda ke mafaka a kasashen Chadi da Kamaru.
Sanarwar hukumar ta kuma yaba wa hukumomin MDD da na kungiyoyi masu zaman kansu na duniya wadanda suka samar da wuraren kwana tare da daukar nauyin abinci da wuraren da 'yan gudun hijirar suke zama. (Suwaiba)