in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta karyata rahoto game da daukar sojojin haya don yakar Boko Haram
2016-11-11 09:48:29 cri

Helkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahotannin dake cewa, an dauko hayar sojoji daga kasashen waje domin amfani da su wajen yaki da Boko Haram.

Wasu kafafen yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa, an dauko hayar wasu sojoji daga ketare domin ci gaba da yakin da dakarun kasar ke yi da mayakan Boko Haram.

Da yake mai da martani game da rahoton, mai magana da yawun helkwatar tsaron Najeriyar Rabe Abubakar, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wannan rahoto karya ce tsagwaronta, kuma babu kamshin gaskiya kan rahoton. Ya ce, dakarun Najeriya suna da karfi, da kuma kwarewar da za su iya rusa duk wata maboyar 'yan ta'adda dake fadin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China