in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata fashewa ta haddasa mutuwar mutane 100 a Cotonou
2016-09-09 19:09:42 cri
Rahotanni daga Benin na cewa, wani abu da ya fashe a wata matattarar kona shara a jiya Alhamis a Cotonou,babban birnin Benin ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 100 kana wasu fiye da 200 kuma suka jikkata.

Wata kafar talabijin mai suna Canal3 ta ba da rahoton cewa, fashewar ta samo asali ne daga rububbiyar filawa da ba ta gama konewa a filin da ake kona irin wadannan shara ba kimanin kilomita 20 arewa da birnin Cotonou.

Rahotanni na bayyana cewa, mutane da dama sun jikkata a lokacin da jama'a ke ribibin kwasar filawar da ta rube, bayan da jami'an da ke sanya ido sun bar wurin da ake kona sharar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China