in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta yi watsi da rahoton MDD game da yadda dakarunta ke cinikayya ba bisa ka'ida ba Somaliya
2016-11-07 09:59:20 cri
A jiya ne mahukuntan kasar Kenya suka yi watsi da wani rahoto da MDD ta fitar cewa, dakarun kasar suna da hannu a fataucin gawayi da ake yi ba bisa ka'ida ba daga wata tashar hakar gawayi da ke karkashin ikon kasar Somaliya.

Kakakin majalisar dokokin kasar Kenya Manoah Esipisu ya yi Allah-wadai da wannan zargi da kakkausar murya,yana mai cewa, wannan magana ce maras tushe.

A jiya ne jaridar Kenya daily, ta wallafa rahoton da wata kungiyar sa-ido ta MDD ta fitar,wanda ke cewa dakarun Kenya da ke Somaliya suna karbar na goro, inda suke barin wasu mutane suna fitar da gawayi daga tashar Kismayu da ke kasar Somaliya ba bisa ka'ida ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China