A jiya Talata rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar damke mutane 9 wadanda take zargi da taimakawa kungiyar Boko Haram, kawo yanzu adadin mutanen da ake zargi da agazawa kungiyar wadanda suka shiga hannun jami'an tsaron kasar su kai 30 cikin kwanaki biyu.
Wata sanarwar da kakakin rundunar sojin Najeriya Sani Usman ya sanyawa hannu ta ce, da farko an cafe mutane 21 ne masu tallafawa kungiyar ta Boko Haram, kafin wannan kamen na baya bayan nan.
A cewar sanarwar, daga cikin wadanda aka damke, biyu jami'an soji ne, biyu jami'an 'yan sanda, sannan ragowar mutane 26 fararen hula ne.
Rundunar sojin ta bayyana mutane da cewa bara gurbi ne wadanda ke kokarin mayar da hannun agogo baya a yunkurin da kasar ke yi na murkushe mayakan Boko Haram.(Ahmad Fagam)