A jiya Laraba gwamnatin Najeriya ta bude kofa ga mayakan kungiyar Boko Haram wadanda ke da muradin ajiye makamansu, bayan da dakarun Najeriyar suka yi barin wuta a maboyar mayakan dake dajin Sambisa a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.
Kwamandan rundunar sojin saman kasar Sadiq Abubakar ya bayyana cewar, sojojin saman Najeriyar suna ta kokarin murkushe 'yan ta'addan domin tabbatar da zaman lafiya a arewa maso gabashin kasar.
Bugu da kari, dakarun Najeriyar sun hallaka mayakan Boko Haram 2 a lokacin wani simame da suka kaddamar a kauyukan Ladin Buta da Juwano dake yankin Jere a jihar Borno.
Kakakin rundunar sojin kasar kanal Sani Usman, ya ce, sojojin kasar na ci gaba da farautar 'yan ta'addan, wadanda ke addabar jama'a da kaddamar da hare hare kan mazauna yankunan tare da hallaka jama'a, da yin garkuwa da mutane da kuma yin fashi da makami a yankunan.(Ahmad Fagam)