A jiya ne, aka rufe kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta Asiya da yankin tekun Pasific wato APEC a birnin Lima, babban birnin kasar Peru.
Sanarwar Lima da aka zartas da ita a yayin taron ta alamta muhimmin matakin da aka dauka wajen aiwatar da kiran da kasar Sin ta yi na kafa shiyyar yin ciniki ba tare da shinge ba a nahiyar Asiya da yankin tekun Pasific. Sa'an nan kuma, a cikin sanarwar, mambobi 21 na kungiyar ta APEC sun nanata himmantuwa wajen cimma burin kafa shiyyar yin ciniki ba tare da shinge ba a nahiyar Asiya da yankin tekun Pasific, tare da mayar da shiyya a matsayin wata muhimmiyar hanyar zurfafa hadin gwiwar tattalin arzikin yankin da kungiyar APEC take ciki. (Tasallah Yuan)