A jiya ne gwamnatin kasar Sin ta mika wa gwamnatin kasar Zimbabwe motoci da kayayyakin yaki da masu farautar namun daji, a kokarin da gwamnatin kasar ta Zimbabwe ke yi na yaki da masu farautar namun daji a kasar.
Sauran kayayyakin sun hada da motocin kallon namun daji guda 10 da a kori-kura guda 7 da manyan motoci 8, katafila guda 10 da taraktoci guda 8 da radiyon oba-oba sama da 100 da tantuna da fitilun tocila da kayayyakin sintiri da sauransu.
Za a yi amfani da wadannan kayayyakin ne a gandun dajin Hwange na kasa da dajin shakatawa na Mana, daya daga cikin wuraren tarihi na duniya da ke yankin arewacin kasar, ta yadda za a kare giwaye da sauran namun dajin da ke daf da karewa a doron kasa.
A yayin da yake mika kayayyakin, jakadan kasar Sin a kasar Zimbabwe Huang Ping ya ce, kayayyakin za su taimaka wa kokarin da Zimbabwe ke yi na kare namun daji. Yana mai cewa, kasar Sin a matsayinta na aminiyar kasar ta Zimbabwe a shirye take ta taimaka mata a yakin da take yi da masu farautar namun daji.
Wadannan kayayyaki wani bangare na yarjejeniyar da shugaba Xi Jinping ya sanya hannu a lokacin da ya kawo ziyara kasar a makon da ya gabata.(Ibrahim)