Mista Moller ya bayyana hakan ne a jiya Talata 25 ga watan nan, a madadin babban sakataren MDD Ban Ki-Moon, lokacin da sabon jakadan kasar Sin na dindindin a ofishin MDD dake Geneva mista Wu Hailong ya gabatar da takardar shaida ta cikakken ikon gudanar da aiki.
Moller ya taya mista Wu murna, tare da yi masa maraba, ya kuma yi godiya game da goyon bayan da tawagar kasar Sin ta nuna wa ofishin MDD dake Geneva, da ayyukan sa baki daya. Kazalika ya yi fatan cewa a nan gaba, kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar harkokin duniya.
A nasa bangaren, mista Wu ya bayyana cewa, a yanayin da ake ciki yanzu, akwai bukatar tabbatar da kwarjinin MDD da matsayin hukumomin ta. Ya ce a koda yaushe kasar Sin na yin tsayin daka wajen goyon bayan ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da mara baya ga kiyaye muhimmin matsayin da MDD ke dauka kan harkokin duniya. (Bilkisu)