Ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya za su tsunduma yaji aiki a ranar Alhamis, a cewar wata sanarwar kungiyar da aka fitar a ranar Alhamis da ta gabata, inda suka bayyana rashin girmama tanade-tanaden dake cikin yarjejeniyar da a karon farko gwamnati ta sanya wa hannu.
Sanarwar da Felix Faniran, shugaban kungiyar ma'aikatan lafiya ta Najeriya (NUAHP) ya sanya wa hannu ta bayyana cewa, kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan an kasa warware matsalolin tare da gwamnati.
Kungiyar ta aike da wata wasikar bin umurni ga dukkan mambobinta, har ma da ma'aikatan sayar da magunguna, kwararrun dake dakunan gwaje gwaje, masu ba da jinya da sauransu dake jahohin Najeriya talatin da shida, in ji sanarwar.
An daidaita wasu matsaloli, yayin da kuma gwamnati ta yi biris da wasu da gangan, a cewar wannan sanarwa, tare da nuna cewa, gwamnati ta kafa wasu kwamitoci domin warware matsalolin, amma duk wani kokarin ya kasa aifuwar da mai ido.
Da farko, kungiyar NUAHP ta baiwa gwamnatin Najeriya lokaci har zuwa ranar 30 ga watan Satumba domin warware matsalolin, amma hukumomin kasar suka bukaci kungiyar da ta jira sakamakon kwamitoci. (Maman Ada)




