Hukumomi a kasar Tanzaniya sun sanar a Lahadin nan cewar, za su hana amfani da ledodi masu lahani ga muhalli.
Ministan muhalli na kasar January Makamba, ya ce, sun aro wannan dabara ce daga makwabciyar su kasar Ruwanda, wanda ta jima da samun nasarar haramta amfani da ledodi masu illa ga muhalli.
Makamba ya ce, tuni ya umarci jami'ai a hukumar kula da muhalli ta kasar NEMC da su bullo da wani shiri don tunkarar magance matsalar zubar da ledodi barkatai a kasar.
An haramta amfani da ledodi ba bisa ka'ida ba a kasar Rwanda ne, tun a shekarar 2008, a yayin da sauran kasashen duniya ke yunkurin sanya haraji ga masu ta'ammali da ledodi, kasar Rwanda, ta yanke shawarar hana amfani da ita ne a kasar.(Ahmad Fagam)