in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban Tanzaniya ya kafa sabuwar majalisar zartaswa
2015-12-11 09:30:44 cri

Sabon shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli, a jiya Alhamis, ya kafa sabuwar majalisar zartaswa mai kunshe da ministoci 19 da mataimakan ministoci 16, adadin da ya kai rabin na gwamnatin da ta gabata kawai.

Gwamnatin da ta shude karkashin tsohon shugaban kasar Jakaya Kikwete na da adadin ministoci da mataimakan su kimanin 60, shugaba Magufuli ya amshi ragamar mulkin kasar ne a ranar 5 ga watan Nuwambar wannan shekara.

Dama dai shugaban ya sha nanata batun rage yawan ministocin a matasyin wani mataki na tsuke bakin aljihun kasar.

Sai dai ya bayyana cewar, har yanzu yana yunkurin zakulo sunayen wasu jami'ai 4 da zai ba su mukamai a ma'aikatun kudin da albarkatun kasar da yawon bude ido da ilmi da sufuri da kuma ma'aikatar sadarwa da kimiyya da fasaha.

Shugaban Magufuli ya amince ya yi aiki tare da ministoci 7 kacal na tsohuwar gwamnatin, inda ya sauke ministoci da mataimakan su 53 na gwamntain da ya gada.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China