in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Tanzaniya za su halarci bikin baje kolin Sin
2016-07-25 10:33:58 cri

Asusun kamfanoni masu zaman kansu na kasar Tanzaniya wato TPSF ya bukaci kamfanonin kasar da su halarci bikin baje kolin kasa da kasa kan hanyar siliki ta ruwa ta karni na 21 da kasar Sin za ta shirya a shekarar 2016 a jihar Guangdong.

Godfrey Simbeye, shi ne babban daraktan TPSF, ya fada cewar, bikin baje kolin na kasar Sin wata babbar dama ce ga kamfanonin kasar Tanzaniya, inda zai ba su sabbin damammaki wajen samun bunkasuwa a fannin kasuwancinsu.

Ya ce, irin makamancin wannan bikin baje kolin, ana gudanar da shi a Dar es Salaam, kana ana sa ran gudanar da wannan bikin baje kolin na kasa da kasa ne a ranar 27 ga watan Oktoba a birnin Dongguan dake lardin Guangdong, a kudancin kasar Sin, inda za'a tanadarwa 'yan kasuwan da suka halarci bikin otel na tsawon kwanaki hudu, da kuma kyautar motocin sufuri daga otel din zuwa dandalin baje kolin.

Simbeye ya ce, wannan wata babbar dama ce ga manya, da kanana, da kuma matsakaitan kamfanonin kasar Tanzaniya, inda za su koyi sabbin dabaru daga mahalarta baje kolin daga kasashen duniya dabam dabam.

Ya kara da cewar, kamfanonin Tanzaniyar za su yi amfani da wannan dama domin tallata kayyayyakin da suke samarwa, da kuma kulla hulda da abokai da sauran masu zuba jari.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China