Wakilin musamman na kasar Sin game da sauyin yanayi Xie Zhenhua, ya ce Sin za ta ci gaba da tallafawa yunkurin kasashe masu tasowa na magance matsalar sauyin yanayi.
Mr. Xie ya kara da cewa, hadin gwiwar kasashen kudu maso arewa, da na kudu maso kudu, na da matukar tasiri wajen bunkasa huldar kasa da kasa a fannin tunkarar matsalar sauyin yanayi.
Jami'in wanda ya bayyana hakan, yayin da ake ci gaba da gudanar da taron sauyin yanayi na duniya a birnin Marrekech na kasar Morocco, ya ce, Sin na daukar nagartattun matakai na shawo kan matsalar sauyin yanayi, tana kuma fatan ci gaba da musaya tsakanin ta da sauran masu ruwa da tsaki.
A cewar Mr. Xie, Sin na tallafawa kasashe masu tasowa da kayayyakin agaji gwargwadon bukatar su, kamar su fitilu marasa bukatar lantarki mai yawa, da murahun girki dake amfani da makamashi mai tsafta.
A daya hannun kuma, Sin ta rattaba hannu kan yarjeniyoyi har 27, wadanda suka shafi tallafawa kasashe marasa karfi, wajen aiwatar da matakai, da gudanar da shawarwari tare da musaya, duka dai da nufin cimma nasarar da aka sanya gaba.
Dandalin tattaunawar da kasashen Sin da Morocco, tare da hadin gwiwar MDD suka shirya, ya samu halartar ministoci da wakilai daga kasashen sama da 10, baya ga jami'an MDD, ana kuma sa ran zai ba da damar gudanar da shawarwari, na zakulo hanyoyin samar da karin kudade, da dabarun wanzar da ci gaba mai dorewa, a yunkurin da ake yi na magance tasirin sauyin yanayi.(Saminu)