in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmai sun yi Allah wadai da harin ta'addanci a Saudiyya
2016-07-06 12:51:59 cri

Kungiyar raya ilmi da kimiyya da al'adu ta addinin musulunci ISESCO, ta yi Allah wadai da hare-haren ta'addanci na ranar Litinin da aka kaddamar a kasar Saudi Arabiya.

ISESCO, wacce ke da helkwata a Rabat na kasar Morocco, ta yi Allah wadai da wannan mummunan hari wadanda ke neman tunzura zaman lafiyar musulmi masu bautar Allah a cikin wannan wata mai tsarki na Ramadan, ta ce, wannan ya saba da karantarwar addinin Islama.

Sanarwar ta bayyana cewar, wadanda ke daukar nauyi, da masu kaddamar da wannan danyen aiki ba su da alaka ta kusa ko ta nesa da addinin musulunci.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta bayyana cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa, niyyar wadannan 'yan ta'adda ba ta tsaya kadai ga kasar Saudiyya ba, har ma tana burin cutar da musulmin duniya baki daya.

Sanarwar ta kara da cewar, duk wani yunkuri na kaddamar da harin ta'addanci kan al'ummar musulmi a masallatai masu alfarma da kuma lokacin wata na Ramadan mai tsarki, da masallatan manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam dake biranen Makka da Madina, halayyace ta makiya musulunci da musulmi, wanda kuma aikata hakan ya ci karo da koyarwar addinin musulunci.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v MDD ta yi tur da harin ta'addanci a Saudiyya 2016-07-06 12:42:26
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China