Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da hare-haren ta'addanci a kasar Saudiyya, wadanda aka kaddamar a daidai lokacin da al'ummar musulmi ke shirye shiryen gudanar da bukukuwan sallar Idi bayan kammala azumin watan Ramadan na bana.
A ta bakin mai magana da yawunsa, Ban ya yi tur da hari-e-haren na ranar Litinin wadanda aka kai a biranen Jeddah, da Qatif, da kuma Madina, hare-haren sun yi sanadiyyar hallaka mutane hudu.
Babban jami'in MDD ya bayyana juyayi ga iyalan wadanda hare-haren suka rutsa da su, da al'ummar kasar ta Saudi Arabiya, sannan ya yi fatar samun sauki ga wadanda suka samu raunuka a sanadiyyar hare-haren.
Ban, ya bukaci a bankado wadanda ke da hannu a hare-haren domin hukunta su, kana ya bukaci a hada karfi da karfe wajen yaki da ta'addanci a duniya baki daya.(Ahmad Fagam)